- |
- |
YADDA ZAKA SAITA SUNA DAYA WATO (SINGLE NAME) A FACEBOOK DA WAYAR ANDROID:
Dubada yanda mutane suke bibiyata da wannan tambayar yau na yanke shawarar rubuta takaitaccen darasi domin ganin duk wanda ke da sha'awar amfani da suna daya a facebook yayi nasarar biyan bukatarsa.
dafarko da kasani facebook ba kowa suke bawa daman saka single name ba sai wanda yake indonssia ko kuma india wato a yankin tamil.
sabida haka ne idan kaje saka suna daya bazasu kyaleka ba domin suna tantance irin network dinka da kuma wurin da kake muddin ba'a wadannan wuraren kake koda network dinsu kake aiki ba tofa bazasu baka dama ba, sai in kayi wasu settings dinda zai nunawa na'urarsu cewa awadancan yankunan kake.
Yanda zakayi Wadannan settings din.
Dafarko dai zakayi amfani ne da chrome ko mozilla firefox sai kuma ka saita yaren facebook dinka ne Zuwa bahasa indonessian daga nan kuma saika saita proxy configuration na indonessia akan wayarka, duka wadannan zakayi su ne ta hanyar searching a google kamar haka (indonessian) proxy server zasu baka result kamar haka:
ko kabi wannan link din domin daukowa kai tsaye https://www.proxynova.com/proxy-server-list/country-id/
shi kuma zama ganshi kamar haka:
sai kaduba nasama kowanne kaza6a daga ciki kakwafeshi domin kuwa shine
wanda zaka saita akan wayarka tahanyar shiga setting>mobile network cellular network >sai kuma access point -> new access point ,
1. Name kasa (my web)
2. kalura dakyau a wajen Apn sai kasa
( Indonessian Network)
3. proxy server sai kasa wannan proxy dinda ka kwafe a google search amma kacire lambobi hudu na karshe.
misali
(124.81.123.2)
4. inda akace proxy port saika saka lambobi hudu daka cire acikin box nasama.wato (8080)
5. sai kuma proxy adress sai kasa (m.facebook.com) sai kayi saving ka tabbata yayi kanar haka:
0 comments: