- |
- |
Whatsapp Zasu dakatar da Account Din Masu Aiki da Third-party Apps.
Kamfanin shaharrariyar kafar sada zumunta ta whatsApp ta yanke shawarar dakatar asusun dukkannin wadanda suke amfani da whatsapp din tahanyar aiki da wani application na daban wanda ba asalin whatsap din ba.
Kamfanin whatsapp zata dauki wannan matakin ne sakamakon ambata wadannan apps din datayi amatsayin mai rashin tsaro da kuma rashin sirri na wadannan applications din da ake aiki dasu.
Wadannan applications din da ake kira Third party apps sun hada da, Gb- Whatsapp, Yo-Whatsapp dadai makamantan irin wadannan apps din.
Kamfanin ta bayyana kudurinta ne na dakatar da wadannan apps din tareda tsaurara bincike akan duk wanda suka samu yana aiki da wadannan app din zasu goge account dinsa na 'yan wasu lokaci daga bisani Su bashi damar komawa cikin account din nashi.
Sabida hakane suke bama duk wani wanda yake aiki da wadannan apps din da ake kira whatsapp third party apps da ya sauya whatsapp din ta hanyar gogeta daga cikin wayarsa sannan yasaukar da ainihin whatsapp din kai tsaye daga playstore, ta hakane kawai zaka samu damar dawo da duk wanda chat history dinka da duk wasu abubuwan dake kan whatsapp account din naka.
Kamfanin whatsapp din dai basu bayyana lokacin da zasu dauki matakin dakatar da asusun masu aiki da third party apps din ba, sai dai suna gargadi ga masu aiki dashi kai tsaye suna iya wayan gari sukalli account dinsu na whatsapp akulle...
0 comments: