Saturday, March 16, 2019

Yanda zaka Sauke video daga youtube kaitsaye batareda wani Software ba.

-
-





Yanda zaka Sauke video daga youtube kaitsaye batareda wani Software ba.







Barkanmu da warhaka kai tsaye yau nazo muku da takaitaccen darasi akan yanda zaku iya sauke video kaistaye daga daga youtube akan wayoyinku ko kuma computer batareda kun wahala wajen amfani da wani software ba.

Ita wannan hanyar dai ba sabon abu bane domin kuwa wasu sun jima da saninnta wasu kuma basu sani ba.
Wannan shine dalilin dayasa naga yadace na dauko wannan darasin sabida wadanda basu sani ba daga cikinmu su amfana dashi, domin kuwa sauke video kai tsaye daga youtube yana bayar da wahala ga wadanda basu sani ba,  wasu kuma suna iya amfani da wasu apps din wajen sauke video din saidai yakan basu wahala kuma zaka iya samun video din yazo musu ba'a yanda suke so ba.

Zanso ka karanta wannan darasin domin saukarda video mai haske daidai yanda kake bukata.

Dafarko dai ka samu browser ko wanne iri, kama daga opera, uc browser, chrome, Firefox da sauransu.
Zaka iyayi a kowanne irin waya ko computer.

Idan kabude browser dinka kai tsaye kaje shafin youtube ta hanyar danna www.youtube.com ko youtube.com awajen saka Url na browser dinka.



Idan yakai ka shafin youtube saika duba wajen searching na video saika rubuta sunan video dinda kake nema,

Misali
Dadin kowa sabon salo.


Idan kasameta sai kabude video din kamar dai zaka kalli video sai ka duba sama wajen saka url wato adreshin shafi zaka ganshi kamar haka:

https://m.youtube.com/watch?v=OSPkrl0VSc8&itct=CBgQpDAYACITCJmPhpz-huECFUuDfAodVv0P61IVZGFkaW4ga293YSBzYWJvbiBzYWxv&hl=en&gl=NG&client=mv-google

Sai taba wajen https://m.youtube.com wato farko daga kan m. Sai kasaka (ss)
Misali:
https://m.ssyoutube.com/watch?v=OSPkrl0VSc8&itct=CBgQpDAYACITCJmPhpz-huECFUuDfAodVv0P61IVZGFkaW4ga293YSBzYWJvbiBzYWxv&hl=en&gl=NG&client=mv-google

Kamar dai yanda yake ahoton nan.


Sai kayi go.


Zai kaika wani shafi dazaka ganta kamar haka:



Anan zasu baka daman za6ar kalan format din da kake so.

Zakagansu kamar haka:
Wbm
Mp4
Mp4
3gp
Sai kaduba kaza6i wanda kakeso kayi click akai ,  kai tsaye za kayi download dinta.
Shikenan




Share This
Previous Post
Next Post

1 comment: