Thursday, May 2, 2019

Dan wasan Kwallon kafa Ronaldo yasayi Mota Mafi Tsada a Aduniya..

-
-








Shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kungiyar kwallon kafa ta juventus dake kasar italiya wato Cristiano Ronaldo yasayi mota mafi tsada aduniya me suna BUGATTI_LAVOTURE_NOIRE kirar kamfanin french luxury.

Wanda aka gabatar da ita  acikin bikin gabatarda sabbin motoci na duniya ashekerar a 2019.



Motar ta kasance mafi tsada aduniya yayinda aka bayyana farashinta amatsayin (£9.49Millions) wato kudin england  pounds miliyan tara da digo arba'in da tara.
Wato kudin spain (€11 million)  euro miliyan sha daya.
Dalar amurka kuma miliyan sha biyu da dubu dari uku da sittin da hudu da dari tara. ($12,364,900).
Idan aka kiyasta ta da kudinmu ta nan najeriya Adadadinta yakai Naira Biliyan hudu da miliyan dari hudu da saba'in da biyu da dubu dari uku da chasa'in da tara da dari bakwai da hamsin (N 4,472,399,750)






Kasantuwar motar ita ce kirata farko a irin nau'inta a duniya,  jama'a da dama sun sanya idanu domin ganin wanene Zai Mallaki wannan motar har ake yada jita-jatan cewa tsohon shugaban kungiyar volkswagen mai suna Ferdinand Piech.
Sai daga baya rahotanni suka bayyana fitaccen zakaran kwallon kafa Ronaldo amatsayin wanda yasayi ita wannan motar.

Sai dai kamfanin ta bayyana cewa wanda yasayi wannan bazai fara Hawanta ba har sai anshiga shekarar 2021 sakamakon kara tabbatar da wasu nau'o'i masu inganci dake cikinta kamar yanda Rahotanni suka bayyana.

Share This
Previous Post
Next Post

0 comments: