Wednesday, May 8, 2019

Wasu Boyayyun Sirrin Kasar Korea Ta Arewa Da Bamu Sani ba

-
-






Wasu Sirrukan Kasar North Korea Wadanda Ya kamata kasani





Shin wane irin Sani kayiwa kasar korea ta Arewa amatsayinka na dan Najeriya?

Takan iya yiwuwa kasan wasu abubuwa da yawa dangane da kasar amma ba lalle bane yazama kasan wadannan sirrukan na ita wannan kasar.
Wasu sirrukan Sunada Matukar ban tsoro da kuma tsauri, wasun kuma suna da ban dariya. Wasun abin ban haushi kazalika wasu sirrukan abin burgewa ne.

Zanso ku biyoni cikin wannan Rubutun domin karanta wasu sirrukan Kasar wanda yakamata ace kasani babu mamaki wata rana ka tsinci kanka akasar.


1 Yanzu Haka ba 2019 Bane .
Mutanen kasar Korea Ta arewa basa bin kalanda irin wanda kasashen duniya ke amfani dashi harma da makwabciyarta korea ta Kudu (south korea) suna aiki ne da wannan akidar na kin aiki da kalandar da duniya take amfani dashi.
Kasashen biyu korea ta arewa da ta Kudu suna aiki da kalandar su ne tahanyar amfani da ranar haifuwar wani tsohon shugabansu Wanda ake kira da suna Kim II-Sung's wanda aka haifa a aranar 15/04/1912 bisaga yanda suka dauki kim II-sung amatsayin shugaba mafi jinkai da kuma kishin kasarsa da ya kafa tarihin wanda basu taba samun tamkarsa ba kasantuwar a lokacin shi wannan shugaban nasu kasashen biyu ahade suke wato koriya ta kudu da koriya ta arewan hakan yasa suke watsi da kalandar da sauran kasashe ke aiki dashi suka rungumi wannan amatsayin nasu.
idan muka dubi yanda tsarin kalandarsu take zamu fahimci yanzu hakayanzu haka a lissafinsu ba 2019 suke ba, suna shekarar 108 bayan ranar Haifuwar Kim II- sung.
Wani abin ban dariya idan haifuwa yazo daidai da ranar da aka haifi Shugaba kim II-sung Ya haramta ayi murnan zagayowar haifuwar wanda aka haifa awannan ranar.


Hukunci mafi Tsauri



kasar koriya ta arewa ta kasance daya daga cikin kasashe masu hukunci mafi tsauri a duniya.



Idan aka kama mutum da laifi akasar korea ta arewa akan hadashi da 'yan uwansa na jini a turasu prison, misali, uba, ko uwa ko kuma yaro idan wani daga ciki yayi laifi takan iya shafan dukkannin 'yan uwansa ta hanyar kama mai laifi da iyalansa a turasu gidan yarin.



99% din jama'ar kasar sunyi karatu



Kiyasin wayewar kasar koriya ta kudu daidai yake data kasar amurka kaso casa'in da tara na mutanen kasar sunyi karatu sosai kuma suna amfana dashi, dukda cewa karatu akasar yanada matukar wahala amma hakan bai hana mutanen korea ta arewa karatu ba.






karancin amfani da Kafofin Sadarwa ta Zamani.



Akasari mutanen korea sam basu damu da shiga shafukan yanar gizo ba ko kuma dai suna da wata doka wacce ta iyakance yanayin aiki da kafofin sadarwa na zamani kamar yanda masu bincike suka bayyana cewa duka mutanen da ke amfana da social networks basu wuce mutane dubu dari ba, Wanda hakan ko 0.05% na mutanen kasar bai kai ba.
Haka zalika sauran kafofin sadarwa wanda ba online ba shima mutanen north korea basu cika mora ba, akwai batun da yake nuni da cewa duka Tashoshin talabijin dinsu a akasar guda uku ne kacal, yayinda sukan bude biyu daga ciki a kowanne ranaku biyu na karshen mako, Dayan kuma kullum sukan budeta da yammacin kowanne rana.

Saka Wando Blue jeans ya Haramta


Kasar Korea ta Arewa Ta dauki kasar america amatsayin babban abokiyar gabarta Shiyasa ma ta ke sanya doka mai tsauri akan duk wani abinda ya danganci america da zai shigo cikin kasarsu.
Kasantuwar Kaya jeans yasamo asaline daga kasar amurka kuma sun lura akwai alamun tambarin kasar amurka ajikin jeans shiyasa kasar korea ta hana amfani da jeans sabida a cewarsu yin amfani da jeans tamkar koyi ne da kasar america wacce ta kasance babban abokiyar gabansu.


Shan giya Haramun ne

Akwai doka mai Tsanani akan Masu shan giya da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi a kasar korea ta Arewa Saidai wani abin ban Haushi shine babu wata doka data hana shan tabar wiwi da makamantarsu akasar.


Birnin Boge: Kijong-dong


Kijong-dong ta kasance birni mai girma wanda take da manyan-manyan gine gine sai dai abin ban dariya babu wani gida da mutane ke ciki acikin wannan birnin, akwai batun dake cewa wasu gidajenma ko dakuna babu acikinsu, ita wannan birnin na Kijong-dong Shugaban kasarsu na yanzu ne yaginata wato kim-Jong Sabida burga tareda nunawa Takwaransu Korea ta kudu (south korea) cewa Sun samu cigaba sosai.



Gwamnatin Kama Karya

Kasar korea takasance kasar datake aiki da tsarin Demokratiya wanda suke zabe a bayan kowanne shekaru biyar.
Sai dai yanda tsarin zabensu yake y bambanta da sauran kasashe, su ba jam'iyya ake amfani dashi ba, sunan Dan takarar Suke rubutawa akan takardan zaben ta yanda idan anje zabe za'a dangwala sunan ne kawai haka zalika sunan dantakara daya tak suke rubutawa akan takardan idan bazaka zabeshi ba sai kaja alamar cross akan sunan dan takaran hakan shine alamar baka sonshi kenan.
Wasu Mahukunta sunyi iya bakin kokarinsu domin sauya wannan tsarin amma abin ya citura daga karshe dai hakan yayi sanadiyar daukan mataki akansu yayinda aka bayyanasu amatsayin masu kawo cikas ma dokokin kasar.

Sun taba Sace wani Shahararren Me bada Umarni daga ma kwabciyarsu South Korea domin gudanar da wani Film

Bisa dukkan alamu shugaban Kasar Korea ta Arewa yakasance mai goyon bayan shirin film sosai, kasancewar rashin kwararrun masana film akasar hakan ne yasa ya tura aka sace wani shahararren darekta maisuna (Shin Sang-ok) Tareda tilasta mishi kayatar musu da wani film dinsu mai suna (pulgasari) shekaru takwas yayi yana aiki akarkashin gwamnatin Korea ta Arewa daga bisani yayi nasarar tserewa a lokacin da suke bukukuwan Film a birnin Vienai.

ba'a barin masu yawon bude ido sui amfank da wayoyinsu.


Eh kwarai kuwa idan kaje bakunta kasar korea ta Arewa tun daga Airport za'a tattara wayoyinku da komai a baku na kasar, sai kungama duk abinda zakuyi kafin nan amayarma kowa wayarsa yayinda yazo komawa,
Kuma koda anbawa bako damar shiga kasar da camera doka ne daukan hoto, ba'a yadda kadauki hoto da talakawa sabida acewarsu daukan hoton talakawa yana rage darajar kasa a idanun duniya.


Duk da wadannan abubuwan kasar korea ta arewa ta cigaba sosai ta hanyar kere-kere wanda yanzu haka sun kai matakin da babu wata kasa da zata nuna masu yatsa batareda sun tanka ba.

Share This
Previous Post
Next Post

1 comment: