Friday, February 15, 2019

Matakan dasuka dace kabi domin yin Rubutu Mai Daukar Hankali a social Media.

-
-













Yanda zakayi Rubutu a social network wanda zai jawo hankalin Mutane.



Shi postin a social media abu ne mai matukar wahala ga wanda bai fahimci sirrin abin ba haka zalika kuma mai matukar sauki ga wanda ya fahimci yanda zaibi wajen tsara posting din.
Kamar yanda muka sani duk wata daukaka da mutum zai samu ashafukan sada zumunta inhar bai kasance celebrity, ko wani dan film ko wani shahararren mutum ba toh zaka samu ya samu daukakar ce ta hanyar tsara posting din abinda ra'ayin mutanensa yafi raja'a akai.

Ta wannan hanyar inada tabbacin zaka buwaya sosai kuma za'a sanka a duniya ta yanda sunanka zai riski inda baka taba tunanin zai iso wajen ba.
Kuma yin hakan yanada matukar muhimmanci domin kuwa idan ka kware wajen tsara rubutun da mutane suke na'am dashi wani lokaci kana zaune za'a kawo ma talla ko sanarwa tayanda zaka watsa a duniya kazalika abiyaka yanda ka bukata, musamman manyan kamfanoni suna yawan bada tallace tallace ga mutane masu jama'a sosai a shafukan sada zumunta wanda kuma zan iya cewa masu yin tallan suna samun kudi mai matukar tarin yawa tahanyar ita wannan tallan.
Haka zalika ita talla tana daya daga cikin hanyoyi mafi kawo kudi ashafukan sada zumunta musamman irinsu adsense, da makamantansu duk talla ne wanda kamfanin google suke bayarwa kuma suke ware wani kaso mai tsoka su biya duk wani wanda suka bashi tallan.

Kada dai nayi ta yin bayani batareda na ta6o kan inda taken darasinmu ta dosa ba.
Wato yanda zakayi rubutun da zai gamsar da masu bibiyarka ashafukan sada zumunta.
Akwai abubuwa masu muhimmanci dasuka dace mu rika kula dasu idan muna yin rubutu na isar da sako ko kuma na nishadi da makamantansu a shafukan yanar gizo.

Abu na farko:

yana da kyau kasani cewa rubutun da zakayi dinnan tana iya isowa ko ina sabida haka yana da kyau ka tattara nitsuwarka kasan abinda zaka rubuta tun daga Farko zuwa karshe kafinma kafara rubutawa yakasance ka gama tantance yanda zaka fitar da rubutun daga farko har izuwa karshe.

Tsara Taken posting

Shi take (title) shi ne abu mafi jan hankalin masu karatu wato yake kwadaita masa jin ya karanta wannan rubutun kuma azahirin gaskiya akasarinmu muna 6ata tsarin rubutunmu ne tun daga title.
Hakika yakamata musani cewa yanayin yanda muka tsara Title na posting din mekyau, iya adadin yawan masu karantawar dazamu samu, domin kuwa ba kowaye bane zaiga taken rubutun da babu ma'ana ya zauna ya6ata lokacinsa wajen karantawa ba, sabida akwai posting dayawa a shafukan yanar gizo tayanda bazai 6ata lokacinsa akan wanda baida alkibla mai kyau ba. Sabida haka saika sa lura sosai wajen tsara Taken rubutunka yakasance kuma baida tsawo shi title din.

Saka Hoto ko Video

Saka hoto yana daya daga cikin abubuwan masu muhimmanci da yakamata ka fahimta idan har ka kasance ma'abocin shafukan sada zumunta domin kuwa shi hoto yana bayyana sakon dake tattare da abinda ka tura a fili ko kuma ince kusan azahirance.
Sai dai kuma bama saka lura inda akasarinmu muke kwafsawa sosai wajen isarda sako ko posting na wani labari haka kawai ta hanyar tura hoto. Misali zakaga mutum zaiyi wani rubutu wanda take dauke da darasi sosai sai kuma kaga yaduba hotonsa da yayi wanka yafita me kyau sai yadaura tareda hoton, sai karasa wanne irin sako yakeson isarwa jama'a? Domin yaraba hankalin me karatu shin hotonka zai tsaya dubawa ko kuma karanta posting dinda kayi din?
Kaga daga nanma kasamu faduwa domin zai kasance sakon da rubutunka ya kunsa bashi ne yake ahoton daka daura ba sabida haka idan har zaka daura hoto yakasance akan abinda hoton yakunsa rubutunka zaiyi bayani.

kalaman Hikima

Yanada kyau amatsayinka na me rubutu kayi taka tsantsan da irin kalmomin dazaka rika rubutawa domin kuwa akwai 'yan sa'ido dayawa wadanda idan kayi daidai bazasu yaba maka ba, amma idan kayi kuskure sai sun kalubalance ka.
Sabida haka idan kayi rubutu kagama kazauna ka karanta dakyau sannan ka fara jin ra'ayin kanka akan rubutun kafin kawatsa ta misali, zaka qaddara cewa wani abokinka ne yayi wannan rubutun sai kaci karo da ita ka karanta shin abin zai birgeka kuwa?
Sai ka duba shin me abin daukar hankali me karatu acikin rubutun ?
Shin wane irin ba'asi (comment) zakayi idan kai kaci karo da irin wannan rubutun?
Kayi tunanin irin yanda ra'ayin mutane daban daban zai dauki posting din dafatan kafahimta?

Takaitawa

Takaita rubutu yana nufin kayi rubutunka cikin kalmomi kadan ma'ana kata6o points na sakon dazaka isar din dukda cewa zakayi amfani da wasu kalmomi masu yunkurar da fahimtar mai karatu tayanda zai fahimceka a sauwake kuma abinda nakeso mugane shi tsawaita rubutu yakan sa mutane suji sungaji da karanta rubutun musamman idan yakasance babu wani gamsassun zantuka acikin rubutun. Sabida haka yanada kyau ka rinka takaita rubutunka tahanyar dunkula sakonka a cikin kalmomi kalilan.

Barkwanci

Shi barkwanci yana nufin kayi amfani da wasu kalmomin da zasu sanyawa mai karatu nishadi tayanda kawai zai tsinci kanshi yana kyalkyalewa da dariya yayinda yake karanta rubutunka idan har me karatu zai rika samun nishadi acikin rubutun ka toh kuwa kullum zai kasance yana bibiyan rubutunka sabida gamsar dashi da kakeyi tahanyar sanyashi nishadi.

Rufewa cikin Hikima

Idan kayi rubutu mai matukar jan hankali akwai bukatar yakasance karufe rubutun da kalaman jan hankali tayanda zakayi amfani da kalmar tsakalarsa tayanda zaiji kawai ka burgeshi,anan anaso kayi amfani da zafafan kalamai idan sakon naka na wani abu ne wanda yake ciwa mutane tuwo akwarya, idan kuma jan hankali ne kayi amfani da tattausan kalamai wanda zai nitsar da zuciyar me karatu.
Idan kuma na nishadi ne sai ka sanya kalmar barkwanci mafi jan hankali akarshe, idan kuma ka koyar da wani abu ne sai karufe da kalmar idan akwai me bukatar karin bayani ya yima comment akasa.

Idan kabi wadannan matakan tabbas zakaga yanda zaka samu karbuwa wajen masu karanta rubutun ka, idan ma baka samun comments zakaga yanda rika samu sosai haka zalika koda acikin blog dinka idan zaka rika sanya wadannan hikimar toh zakaga yanda zaka samu sauyi wajen tara traffic....
Share This
Previous Post
Next Post

0 comments: