Monday, March 18, 2019

Abubuwan Burgewa Dangane da Uc Browser

-
-





ABUBUWAN BIRGEWA DAKE TATTAREDA UC BROWSER...



Wato yau zanyi amfani da kankanin lokacin dana samu wajen nunawa wasu daga cikinmu ingancin yin amfani da uc browser tahanyar rubuta takaitaccen bayani,
wato akasari jama'a nasan wasu sunsan uc browser, matukar mutum yakasance mai amfani da waya📱ko computer 💻 ?wanda take da daman shiga shafukan yanar gizo-gizo 🌐 zaiyi wuya yakasance baisan ita wannan manhaja tashiga shafukan yanar gizon ba, musamman masu harkan zana shafukan yanar gizo-gizon (webmasters) da ma masu gudanar da ayyukan cikinta (bloggers / publishers) a6angare guda kuma dayawa basu san ingancinta ba, kuma basu damu da su sani ba sabida akasarinsu abinda sukeyi a yanar gizo bai wuce shoga facebook dakuma Downloading na wasu abubuwa ba sai kuma wasunmu shiga shafukan labarai wanda yake da nasaba da labaran duniya, rahotanni ko kuma labarin wasanni dasauransu, atakaice dai kowa da irin yanda yake amfani da manhaja ta yanar gizo waje shiga shafukan.
Da farko dai menene Uc browser?
Amsa: Uc browser Wata manhaja ce mallakin kamfanin ucweb wanda a bincikena ya bayyana cewa an kirkireta ne tun ashekarar 2004 akasar china akarkashin wata Kungiyar masana na'ura da shafukan yanar gizo da akeyi mata take da ALIBABA GROUP. Inda aka fara kirkiranta da formati din j2me daga bisani aka kara samun fasaha suka cigaba da inganta abin har yakaiga sun kirikiri na duk wani irin nau'in na'ura musamman wadanda suke amfani tahanyar wadannan format din wato, exe,jar,jad,sisx,sis har Izuwa Apk da sauransu. Tayanda yakasance ana iya samun manhajan na shiga shafukan yanar gizon na kowa ne irin nau'in na'ura da ake amfani dashi, kama daga computer, java phones, symbian phones, Blackberry, Windows Phones, IPhones, Android phones da dai sauransu.
Uc browser takasance daya daga cikin browsers mafi shahara a duniya yayinda akan iya sata amatsayin na 3 mafi inganci biyo bayan browser na Google Chrome da kuma safari.
A shekarar 2014 uc browser ta kasance browser din da akafi amfani da ita akasahen yankin Asia musamman ma india, Pakistan, japan,Indonesia da sauransu.

Wasu ababen birgewa dake tattareda uc browser sun hada da:

Sufficient clipboard 📄
Smart copy and pastes📝📥
themes customization
Uc video player ▶

Dasauran wasu kananun abubuwanda bazan iya tunosu ba.

Bari na dauki abinda yafi burgeni nafara bayani akai wato clipboard.

Clipboard
Idan muka duba clipboard wato ita clipboard wata ma adana ce ta rubutu yayinda idan akayi copy takan adanu ne acikin clipboard sabanin yanda yake asauran browsers duk abinda ka kwafe da zaran kasake kwafe wani zai maye gurbin wancan wanda kayi afarko, toh shi a Uc browser duk abinda kayo copy yakan zauna ne a clipboard ta yanda koda zakayi copy din abubuwa daban-daban zaka samesu a clipboard kowanne da fanninsa, wannan shine dalilin da yasa akasari masu harkan zana shafukan yanar gizo ke amfani da uc browser sabida adana codes da wasu bayanai masu muhimmanci.
Haka zalika ma rubuta ashafukan yanar gizo suma sun bada amanna sosai wajen yin amfani dashi uc browser din.
Domin ko nima nan alokacin danake rubuta labarai a kullum awasu pages na facebook ina matukar jin dadin aiki dashi, sabida idan kayi copy din rubutu a Uc browser koda ka kashe wayarka zaka samesu acikin clipboard idan ka kunnata.
Haka zalika shi adadin harufan da yake dauka ya danganta ne da irin na'uran dakake amfani dashi.
Misali alokacin danake amfani da wayar nokia java phone. Uc browser din jar version 9.5.0.449 da aka sabunta shi a 23 June 2014; Nakan iya adana harufan da suka kai dubu biyar(five thousand characters) acikin, wanda shine iya adadin da uc browser din java phones suke dauka.

Yayinda shi kuma symbian kusan yakasance yana daukan unlimited characters sai kuma shi iya adadinsa yadanganta bisa abubuwa ma banbanta dakayi copy, baya wuce daukan abubuwa ma banbanta sama da hamsin koda kuwa adadin kowanne yakai harufa dubu hamsin ne (50,000 characters) takan dauki kamarsu sau 50 batareda ta nunamaka iya

iyakarta ba, saidai tafara maye gurbin na farko dana karshe. Ita kuma haka take,

Yayinda ita ko na Waya kirar Android wanda aka sabunta ta (upgrade ) zuwa version 12.8.5.1121 aranar ' 17 July 2018 a yanzu watanni 8 kenan dasuka sabunta ta, a iya shige-shigen danayi na amfani da ita bangano iya adadin harufan da clipboard dinta yake dauka ba, haka kuma yake ma a nau'in na computer..

- Copy and pastes


nasan akasari ansan me copy and Paste amma bazaiyiwu ACe kowa yasani ba , Sabida haka zan Danyi takaitaccen bayani gameda copy and paste din Na uc browser kamar yanda muka sani yasha bamban dana sauran browsers , copy wata dama ce da zakayi amfani dashi wajen kwafe Duk Wani Abinda kagani na nau'in files, ko rubutu da sauransu tayanda zaka iya kaishi Duk inda kaga dama ka Ajiye shi awajen tahanyar paste. Bambancin copy and Paste din uc browser dana sauran browsers shine ita uc duk abinda ka kwafe yakan adanu Acikin clipboard tayanda koda kasake kwafe wani Shima yana da daman zama acikin clipboard din batareda ya maye gurbin wancan Wanda Kayi Afarko ba.
Haka zalika koda ka Kashe Wayarka Zaka Samesu Acikin Clipboard Idan Ka Kunnata , kaga kenan tana da matukar fa'ida sosai sa6anin sauran browsers idan ka kashe wayarka shikenan abin da ka kwafe sun tafi.

Themes Costumization

- Shiko Themes customization wata dama ce Da zaka iya saita irin launin Da kake so kaga browser din dashi, akwai themes ma banbanta dake cikin uc browser wanda zaka iya sauya SU izuwa irin wanda kakeso , idan kaga dama ma zaka iya Zana irin themes dinda kakeso kasaita kalan Background dinda ya Dace Da ra'ayinka harma hotonka kana iya sanyawa Acikin browser din amatsayin themes dinka na uc browser .
Night Mode
- shi kuma night mode wanda akayi Shi sabida masu matsalar idanu, tayanda idan kasaita night mode takan sauya launin Browser din gabadaya tamaidashi baki (black) rubutun Cikin kuma tamaidashi grey(ruwan toka) tayanda zai dushar da hasken batareda ta sanyawa idanu illa Ba.

Atakaice dai Akwai ababen birgewa sosai Dake Kunshe Acikin Uc Browser Wadanda bazan iya bayyanosu acikin kankanin lokacin ba .
Sai dai nan gaba idan nasake Samun dama zan kawo karin bayani gwargwadon abinda nasani Akai musamman ma akan wadannan.
Uc video player
Lock screen Smart Charging
Text viewer
Html viewer
Pdf reader
Uc News Updates
Qr code scanner
Desktop ,mobile and Lite Version Of Websites.
Da sauransu duk wadannan wasu abubuwa ne da Uc browser ke kunshe dasu.
Sai ku cigaba da kasancewa da wannan shafin..


Share This
Previous Post
Next Post

0 comments: