Saturday, March 23, 2019

MTN : Yanda zaka sayi plan na kallo a youtube kawai.

-
-















AYanda Zaka Sayi Plan Na kallo a youtube Kawai.


Kamfanin sun kaddamar da wani sabon tsari wanda yake bawa duk wani mai amfani da layin na Mtn damar sayan plan wanda zaiyi amfani dashi wajen kallon video a youtube kawai,
Kamar dai yanda muka sani ana iya sayan data plan na facebook ko na whatsapp kawai dasauransu,
haka wannan tsarinma yake na youtube ne kawai, saidai shi wannan yasha bamban da sauran social plans din.
Shi wannan zakayi kallo ne ayoutube sosai na adadin lokacin da kasaya.


Yanda abin yake


1 zaka iya sayan Youtube plan na tsawon Awa daya (1hr) akan Naira dari da Hamsin (N150) tahanyar tura sakon VP1 zuwa 131.


2. Zaka iya sayan Na tsawon awanni uku (3hrs) akan Naira dari hudu (N400) tahanyar tura sakon VP3 zuwa 131.

3. Domin kuma sayan na dare wato (YouTube Night plan) wanda sai daga karfe 12:00am zuwa zuwa 5:00am zakayi amfani dashi Saika tura VP5 zuwa 131 akan naira hamsin (N50)

Amma fa yanada kyau kasani shi wannan tsarin adadinsa tsawon awanni ashirin da hudu ne kawai wato 24hrs sukeyin expire.

Ribarsa zaka mori kallo a youtube ne na tsawon lokaci batareda kayi tantaman data dinka zai kareba, kawai abin dazaka lura dashi shine lokaci tayanda bazaka shafa'a har adadin lokacin naka yakare ba....



Fatan Alheri.
Share This
Previous Post
Next Post

0 comments: