- |
- |
Hanyoyin da Hackers ke bi Wajen Shiga Facebook Din Jama'a
*
*
*
*
*
*
*
*
Kamar yanda na dauki alkawari ma wasu daga
cikin abokai na masu muhimmanci cewa idan
nasamu dama zan danyi karin haske akan
wadannan matsalolin dasuka addabemu
ashafukan yanar gizo musamman yankinmu na
arewa awannan shekarar abin har yayi matukar
muni,
yayinda kwatsam ake shiga Facebook din mutane
ana sauya musu suna babu gaira babu dalili.
wasu kam abin har yakaiga hallakar account
dinsu.
koma dai menene duk munsani abin baiyi mana
dadi ba, muna ganin yadace ace mun dauki
mataki akai.
yanada kyau ka juri karanta wannnan rubutun
sannan kadauketa da muhimmanci.
idan kasani akwai wadanda basu sani ba.
Menene Hacking
Hacking anawa fahimtar ana nufin kutsa kai cikin wani
abu ta barauniya hanya batareda sanin ma malllakin ita wannan
abin ba.
idan kuma muka duba hacking na facebook shine
kutsa kai cikin shafin wani batareda izininsa ba.
wato abinda yazama ruwan dare awannan zamani da muke ciki kenan.
daga cikin dalilan dasuke sa ayi hacking akwai
mallakar abu mai muhimmanci wanda yake
dauke hankalin dan kutsen har yakwadaitu da
zuwa yakwata koda kuwa da karfin tsiya ne.
shin menene daliln dayasa mu yan arewa akafi
kwace mana shafukan facebook tareda lalata mana su.
Sakachi
Na farko akwai sakaci dakuma ganganci wanda
hakan shike bawa masu kutse daman 80% su
shiga su aikata mana ta'adi yanda sukeso.
sakaci da kuma gangancinmu anan shine rashin
sanin muhimmancin password ko kuma ince
rashin ingantashi misali mutum ne zaka samu
yana amfani da lambar wayarshi amatsayin
password dinshi.
ko kuma kayi amfani da wani bangare na lambar
ka amatsayin password.
bari inbada wani misali agaskiya idan wannan
misali da zan bayar tashafeka sai kayi kokarin gyarawa.
mukaddara inaso zan kutsa cikin account dinka
domin in aikata maka wani ta'adi da farko zanfara jarrabawa ne da lambarka tahanyar
hasashe wato predict aturance ko kuma ince guessing.
Mukaddara kabada damar ganin lambarka a profile dinka nashiga sai nayo copy ace lambarka
itace wannan 09035668852 sai inje wurin login
insaka lambarka tahanyar pasting tunda dama
can nayo copy dinta wurin saka password sai inkuma saka lambarka din.
idan nasamu damar shiga toh fa shikenan idan kuma password dinka ba haka bane sai in cire 090 nafarko insaka da 35668852 insake komawa password dinka ingwada idan hakanma bata yiwuba sai in sake cire lambobi uku na karshe wato insaka daga 09035668 sai ingwada idan hakane madallah idan bahaka bane sai in dubi sunanka sai ingwada amatsayin password misali RILWAN da manyan harufa idan baiyiba sai ingwada da kananan harufa idan hakanma baiyiba sai inkuma dauko karshen lambarka insaka akarshen sunanka misali RILWAN52 zangwada da kananan harufa ma haka. idan baiyi ba hakanma sai in bincika ya yanayin ka yake shin kana yin soyayya ne? ko kanada.aure?
idan amsar eh ne toh shin me sunan budurwarka ko matarka? zanyi kokari ingano duk sabida
kawai insamu damar shiga indebi bayanan danake bukata aciki.
Haka Zanyi ta hasashe har sai na gano kalmar sirrinka, karkaji lokacinda yan kutse ke kashewa domin lalata abinda suka sanya agaba idan har baka tsira daga matakan dana irga dinnan ba tofa yanada kyau kayi kokari kasauya password dinka tahanyar saka symbols aciki da kuma garwaya harufa manyan da kananan lambarka kuwa kaboyeta daga cikin
profile dinka,
idan kayi nasarar magance wadannan toh fa sai dai dan kutse yabi wasu hanyoyin dazanyi bayaninsu badai yayi hasashe ba.
2 forget password
Suna iya shiga Facebook account dinka tahanyar forget
password.
kamar yanda nayi bayani suna iya hasashen gano password na Facebook haka simple suke gano na email atafiyar da muke ciki har anfi amfani da lamba amatsayin password na email fiyeda facebook abin har yazama jiki tayanda akasari wadanda aka bude musu email a cafe zaka samu
lambarsu ne password dinsu. kaga hakan zai bawa dan kutse damar shiga account dinka cikin sauki koda kuwa password dinka yanada wahalarganewa idan yayi forget password shikenan koda kana aiki da approval pin ne.
tura bayanan zuwa gareshi dan kutsen dayasaka ma ita wannan software din.
kaga idan yayi forgot password zasu tura maka confirmation code tayanda dazarar yashiga cikin spy software dinsa zata nuna masa, sai yadauketa yaje yashiga account dinka yayi duk abinda yaga dama.
idan kanason kagane wayarka akwai spy software ko babu sai kaje settings kashiga apps daga nan sai kashiga running services duk wani abinda ba kasan dashi ba sai kayi uninstall dinsa cikin sauki.
ka kuma nemi anti virus dazai rika kula da duk abinda zai shigo cikin wayarka.
3 Phishing
phishin hanya ne mafi shahara da yan kutse suke bi domin samun nasarar kutsawa cikin account
din duk wanda suke bukata.
taya ake phishing?
amsa itace zasu Gina shafi ne mai matukar kama da facebook daga bisani su tura ma wanda
sukeson shiga account din nasa link din ita wannan website din da suka ginan tayanda
dazarar kashiga zai kalleta tamkar Facebook shafin haka zalika zaiga kamar kayi logout na
Facebook dinsa ne domin kuwa zaiga sun bukaci kayi login na Facebook account dinsa ne awajen dazarar kayi login details na account dinka zasu kasance automatically text file kuma sukan iya tsarata zata aika mai details dinka ta email tayanda dazarar sunyi download dinsa shikenan sunyi nasarar samun details dinka kuma hakan zai basu daman shiga Facebook dinka
yanda zaka magance kanka daga sharrin phishing.
na farko shine ka kauracewa duk wani sako dazai shigo email dinka ya bukaci kayi login na
Facebook dinka.
- ba saita email kadaiba haka kwatsam kana iya cin karo dashi makamantan link wanda zaka
gansu kamar facebook idan bazaka iya tantance wa ba yanada kyau karika amfani da chrome
wajen shiga shafukan yanar gizo sabida ita chrome tana tantance phishing site tayanda dazarar zaka shiga zata nuna ma.
4 keylogger
keylogger aduk inda kaji ambaci keylogger wato wata manhaja ce (software) da yan kutse suke kirkira su sanya ta acikin na'urar wanda suke bukata yima hacking din, tahanyar install dinta akan nau'rar tayanda zata rinka daukan duk wani abinda ake aikatawa acomputer din daga bisani ta aika musu bayanan data dauka din adunkule, ta hanyar email ko kuma FTP wato file transfer
protocol.
yanda zaka magance kanka daga sharrin keylogger.
Nafarko shine kayi install na firewall software wanda zata baka damar tantance duk wani abinda zai shigo cikin na'urar ka kama daga online harma offline, aduk sanda wata manhaja ta waya kota computer ke kokarin fitarda bayanan sirri ita wannan firewall software din zata nemi izninka kafin abin yatafi kaga kenan hakan zai baka damar ganin duk wani abinda zai fita daga na'urar ka.
-anti virus mai matukar inganci kuma yakasance updated one wato sabontacce.
- ba kowanne sakone zaka kallesu ta email kabude su harma kayi download dinsu ba, hakan ma yana iya bawa dan kutse damar satar muhimman bayananka yayi awon gaba dasu.
- yakasance kana sauya password dinka lokaci zuwa lokaci. akwai hanyoyin dayawa wadanda zama daya bazasu lissafu ba sabida haka zan dakata anan
RILWAN REALLY 09035668852
0 comments: