- |
- |
YANDA ZAKAYI FREEBROWSING ALAYIN ETISALAT DA HI VPN
Kamar Yanda muka sani cewa Lalle yanzu data yanada matukar wahalar samu, musamman yanayin da muke ciki Na tsadar rayuwa akasamu najeriya Data wanda zamu rika shiga shafukan yanar gizu suna nema su gagaremu sakamakon rashin Nauyi aljihu da kuma al'amuran da muke fama dasu na yau da kullum.
Awannan zamanin da muke ciki shiga shafukan yanar gizo kusan yazame mana wajibi kuma hakan baya yiwuwa dole sai muna da Data.
Ashe kenan data ayanzu ta kasance daya daga cikin ababen da zamu kasance cikin takura idan babu su musamman ma idan muna amfani da wayoyin Hannu na zamanin.
Batareda na cika ku da surutu sosai ba bari naje kai tsaye zuwa kan abin da darasinmu ya kunsa.
Kamar yanda muka sani A wannan lokacin ana yawan samun wasu hanyoyi na morar garabasar free browsing a layukan da muke aiki dasu musamman Mtn da Glo. Toh a yau insha Allahu wannan darasin kai tsaye zamu duba ne yanda zamu samu daman morar freebrowsing maras iyaka (unlimited) tahanyar aiki da layin 9mobile (Etisalat) sabida haka idan ka mallaki Layin etisalat yana da kyau kabi wannan darasin domin kada a mora banda kai.
Dafarko abubuwan da ake bukata sune.
Na farko :
layin Etisalat (9mobile simcard)
Na biyu :
Waya kirar android kowacce iri.
Na uku : Application mai suna HI VPN.
wannan vpn din baida matsala wajen raina network domin kuwa ba lalle bane yakasance sai network dinka yakai 3g ko 4g, shi HI Vpn yana aiki akowanne irin generation daga 2g zuwa sama duk zaka iya aiki dashi.
Sabida haka idan kanada bukatar shi Hi Vpn din Sai ka shiga nan
Bayan kadauko shi kayi installed dinsa akan wayarka sai kabudeshi.
Kashiga ciki tahanyar start.
Zata kaika ciki inda zata nuna maka sunakin kasashe daban daban kamar yanda yake acikin hoton dake kasa.
Kaduba Random location Sai kayi click akai sannan kataba kan Tap to connect.
Zakaga yadauka yafara searching for network configure, waiting for server reply zakaga dai wani alamar gwaigwai yana tafiya sai kadan jirashi zakaga yazo yayi connected
Zaka iya ganin yanuna maka error server, ko kuma failed to connect, ko kuma region is full, duk karka damu kawai kasake reconnect zaiyi, idan ma hakan yacitura sai ka bashi mintuna kamar 15 sai kasake gwadawa insha Allahu zai dauka.
Idan kanason yin amfani dashi a computer kuma sai ka bude hotspot na wayar ka matso da ita kusa da computer din sai ka duba wajen wireless connection ,Zakaga connections are available sai kashiga zakaga connect sai ka taba kai, zakaga yayi connected sai ka bude browser dinka kawai kamore...
Rilwan Really...
0 comments: